Thursday, May 8, 2014

Jirgin Sama Ikon Allah

Baka mamakin yadda idan ka jefa dutse sama komai kankantasa sai kaga ya dawo kasa, amma in ka daga kan ka sama sai ka hango wani katon Jirgi amma bai fado ba? Wannan shine tunani na farko daya fado raina a lokacin da aka bada sanarwar cewar dukkan fasijojin Egypt Air wanda zai tashi daga Kano zuwa Cairo su kasance cikin shiri domin jirgin zai tashi da karfe 12:10 na safiyar ranar Lahadi 2/2/2013.